Zhao Houlin ya bayyana cewa, sha'anin sadarwa yana daya daga cikin manyan sha'anonin da suka sa kaimi ga bunkasuwar zamantakewar al'umma da tattalin arziki na dan Adam, dukkan burin samun bunkasuwa mai dorewa guda 17 dake cikin ajandar samun bunkasuwa mai dorewa ta shekarar 2030 ta MDD suna da nasaba da fasahohin sadarwa. Kawancen yana fatan kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa ta hanyar more fasahohin sadarwa na zamani. (Zainab)