in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin mutanen da suka rasu sakamakon girgizar kasa da ta auku a Mexico ya karu zuwa guda 65
2017-09-10 13:12:30 cri
A jiya Asabar, shugaban hukumar tsaron fararen hula dake karkashin jagorancin ma'aikatar harkokin gida ta kasar Mexico Luis Felipe Puente ya bayyana cewa, adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasa da ta auku a kasar ya karu zuwa guda 65.

A ranar 8 ga wata da yamma, shugaban kasar Mexico Enrique Pena Nieto ya kai ziyarar aiki birnin Juchitan na jihar Oaxaca, wurin dake fama da bala'in, inda ya bayyana cewa, gwamnatin za ta hada kai da bangarori daban daban domin fuskantar wannan bala'i, ta yadda za mu warware matsalolin dake gabammu yadda ya kamata.

Haka kuma, gwamnatin za ta samar da ruwan sha da abinci ga mazauna wurin cikin sauri, tare da yi musu jinya yadda ya kamata.

A ranar 8 ga wata ne, kasar Mexico ta fara zaman makoki na kwanaki 3, inda aka sauko da tutoci duk fadin kasar kasa-kasa, domin nuna juyayi ga wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan bala'i na girgizar kasa da ta aukawa kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China