in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka mutu a sakamakon girgizar kasa da ta auku a kasar Mexico ya kai 58
2017-09-09 13:18:05 cri
Shugaban hukumar kula da ayyukan tabbatar da tsaron jama'a ta ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Mexico, ya bayyana da yammacin jiya cewa, bisa rahoton da kwamitin tunkarar batutuwan gaggawa na kasar ya gabatar, yawan mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa da ta auku a kasar ya karu zuwa 58.

Girgizar kasar mai karfin maki 8.2 bisa ma'aunin Richter ta aukawa kasar Mexico ne a daren ranar 7 ga wata.

Jihar Oaxaca dake kudancin kasar ita ce jiha da iftila'in ya fi aukawa, inda yawan mutanen jihar da suka mutu ya karu zuwa 45.

Baya ga haka, wasu mutane 10 na jihar Chiapas da 3 na jihar Tabasco su ma sun mutu sakamakon iftila'in.

Rahotanni sun bayyana cewa, zuwa yanzu ba a gano manyan tituna da suka lalace a jihohin uku ba, don haka ana iya gudanar da ayyukan farfado da yankunan cikin hanzari. Inda a daya bangaren, ake ci gaba da gudanar da ayyuka a filayen jiragen sama da tasoshin jiragen ruwa na kasar.

Tuni dai shugaban kasar ta Mexico Enrique Pena Nieto, ya je yankunan da iftila'in ya fi yi wa illa a jihar Chiapas, don duba yanayin wurin.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China