Rahotanni daga Mexico na cewa, mutane a kalla 9 ne suka gamu da ajalinsu lokacin da wata girgizar kasa mai karfin maki 8 bisa ma'aunin Richter ta aukawa yankin gabar ruwan kudancin Mexico a daren jiya Alhamis.
Jami'in sashen kula da tsaron jama'a Jose Garcia ya tabbatar da cewa, mutane 7 ne suka mutu a jihar Chaipas lokacin da gidajen suka rufta, yayin da wasu mutane biyu kuma suka mutu a jihar Tabasco mai makwabtaka.
Ita ma hukumar safiyon kasa ta Amurka ta ce, girgizar kasar ta mamaye kilomita 6 a kudu maso yammacin garin Pijijiapan dake jihar Chiapas, kana ta kai zurfin kilomita 33
Shugaba Enrique Pena Nieto na kasar Mexico ya ce an farfado da tsarin daukin gaggawa na kasa, kana an umarci gwamnatocin kananan hukumomi da su sanya ido tare da gudanar da ayyukan ceto. (Ibrahim)