in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD zai mai da hankali kan yaran Afirka a Maris
2015-03-04 10:22:58 cri

Shugaban kwamitin tsaron MDD na watan Maris din nan, ambasada Francois Delattre, ya ce, a wannan wata kwamitin zai ziyarci nahiyar Afirka, a wani mataki na karkata hankulan masu ruwa da tsaki ga halin da yara ke ciki, musamman ma a yankunan da ke fama da rigingimu.

Delattre wanda kuma shi ne wakilin din din din na kasar Faransa a MDD, ya shaidawa wani taron manema labaru cewa, ziyarar ta kwanaki 4, za ta baiwa kwamitin damar sabunta shirin MDD na wanzar da zaman lafiya a janhuriyar dimokaradiyyar Congo ko MONUSCO a takaice. Ya ce, wannan mataki ne da zai jaddada burin MDDr, na ganin an karfafa manufofin siyasa, da wanzuwar tsarin dimokaradiyya a nahiyar ta Afirka.

Ana dai sa ran wakilan kwamitin za su ziyarci kasashen janhuriyar Afirka ta Tsakiya, da Burundi da kuma helkwatar kungiyar AU dake birnin Addis Ababa, tsakanin ranekun 10 zuwa 13 ga watan nan na Maris.

Har wa yau Mr. Delattre ya ce, za a gudanar da wata mahawara game da halin da yara ke fadawa, a yankunan dake fama da tashe-tashen hankula, taron da zai gudana a ran 25 ga wata, wanda kuma ake sa ran zai samu halartar babban magatakardar MDDr Ban Ki-moon.

Ya ce, babbar manufar zaman ita ce tattaunawa, tare da kara kaimi ga aikin yaki da masu tada kayar baya da kungiyoyin 'yan ta'adda, tare da lalubo hanyoyin wanzar da zaman lafiya a kasashen Mali, da Afirka ta Tsakiya. Sai kuma burin da ake da shi na gani bayan mayakan kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a Najeriya da Sham da kuma kasar Iraq. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China