Hukumar raya masana'antu ta MDD UNIDO, ta ba wani yankin na kasar Sin shaidar kasancewa yankin masana'antu marasa gurbata muhalli, al'amarin da ya kawo adadin irin wadannan yankunan a kasar zuwa 5.
An ba da wannan shaida ce ga yankin tattalin arziki da fasaha na Quanzhou dake lardin Fujian na gabashin Sin, wanda ya kasance cibiyar masana'antu dake sarrafa tufafi da takalma da injuna da magunguna da kuma na'urorin zamani.
Yankin na UNIDO, na nufin wani sabon yankin masana'antu dake amfani da kayayyaki da nau'ikan makamashi ake rage tasirinsu wajen gurbata muhalli da rage fitar da dagwalo domin fadada ingancin albarkatu da amfani da makamashi da kuma rage abubuwan dake lalata muhalli daga kayayyakin da ake amfani da su a masana'antun. (Fa'iza Msutapha)