Cibiyar tabbatar da sauyi a fannin tattalin arzikin Afrika dake Ghana ACET, ta bukaci kasashen Afrika su dauki matakan inganta ayyukan masana'antu, don shiga a dama da su a kasuwar duniya.
Cikin wata sanarwa da ta fitar jiya, gabanin taro kan sarrafa kayyayaki da za a yi cikin wannan watan a Addis Ababa, babban birnin Habasha, cibiyar ta ce nahiyar Afrika, ita ce koma baya cikin sauran nahiyoyin duniya wajen sarrafa kayyayaki, kuma a don haka, akwai bukatar inganta ayyukan masana'antu domin samun ci gaba ta fannin zaman takewa da tattalin arziki.
Sanawar ta ruwaito cibiyar na cewa, muddun nahiyar na son shiga a dama da ita a kasuwar duniya, sai ta magance wasu kalubale da ke dogaro da juna.
Cibiyar ta ce, duk da ci gaban da nahiyar ta samu a a shekarun 1960 zuwa tsakiyar 1980, a yanzu ta zama koma baya cikin sauran sassan duniya.
Taron wanda za a yi a ranar 5 ga watan nan, na da nufin kaddamar da tattaunawa kan yadda shugabannin kasashen Afrika za su inganta harkokin masana'antu kamar yadda yake cikin manufofinsu na kawo sauyi. (Fa'iza Mustapha)