in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
BAII zai hadin gwiwa da UNIDO domin tallafawa ci gaban masana'antu a Afrika
2016-11-22 10:00:58 cri

Bankin Asiya kan zuba jari domin ababen more rayuwa (BAII) zai iya yin hadin gwiwa nan da 'dan lokaci mai zuwa tare da kungiyar bunkasa masana'antu ta MDD (UNIDO), da zummar karfafa ci gaban masana'antu a Afrika, in ji mista Jin Liqun, shugaban bankin BAII a ranar Litinin.

A yayin da yake halartar bikin cika shekaru 50 na kafuwar kungiyar UNIDO a Vienna, mista Jin ya bayyana cewa, BAII na raba tare da UNIDO wani aiki guda na bunkasa ci gaban masana'antu cikin karko, kuma zai iya yin hadin gwiwa nan gaba tare da wannan kungiya domin tallafawa ci gaban masana'antu a kasashen Afrika.

Ko da cewa BAII na nuna muhimmanci sosai ga ci gaban shiyyar Asiya, amma kuma nahiyar Afrika na kasancewa yanki mai jawo hankali domin zuba jari.

Shugaban BAII ya bayyana cewa, Afrika na bukatar karin taimako kamar sauran yankuna, misalin yankin Latin Amurka, ganin cewa yawancin kasashen Afrika na dogaro har yanzu musamman ma da albarkatun da suke hakowa. Dalilin haka ne, bunkasa ci gaban masana'antu ya zama muhimmin mataki ga kasashen Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China