Wata sanarwa da aka fitar a shekaran jiya, ta ce kungiyar ta'addanci ta Boko Haram na ci gaba da tada zaune tsaye a jihar Diffa, yayin da 'yan ta'adda na kasashen Libya da Mali ke haifar da barazana ga tsaron yankin Sahel, wanda ya shafi mekeken filin dake yammacin kasar. Kuma wadannan batutuwa ne suka wajabta daukar matakin kara wa'adin dokar-ta-baci a wadannan wurare.
A farkon watan Yulin da ya gabata, 'yan Boko Haram sun kai hari kan wani kauye dake yankin Nguigmi na jihar Diffa, inda suka kashe mutane a kalla 9, tare da sace wasu 45. Haka zalika a karshen watan Yunin da ya gabata, 'yan Boko Haram 2 sun kai harin kunar bakin wake a wata cibiyar tallafawa 'yan gudun hijira dake yankin, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 4, da jikkatar wasu 11.(Bello Wang)