in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasancewar Nijeriya dunkulalliya abu ne mai muhimmanci da ba zai sauya ba
2017-09-17 12:52:40 cri
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya ce kasancewar kasar dunkulalliya abu ne mai matukar muhimmanci da ba zai sauya ba, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ta tanada.

Muhammadu Buhari, wanda mataimakinsa Yemi Osinbajo ya wakilta yayin wani taro da ya gudana jiya a Kaduna dake yankin arewacin kasar, ya bukaci 'yan Nijeriya su kauracewa kalaman kiyayya da na rarrabuwar kawuna da kuma duk wani abu daka iya tarnaki ga hadin kai da kasancewar kasar tsintsiya madaurinki daya.

Shugaban na wannan jawabi ne yayin bikin yaye wasu sojoji da suka kammala karatu da karbar horo a Kwalejin horas da sojoji ta kasar.

Shugaban ya kuma bukaci rundunonin tsaron kasar su gujewa nuna bangaranci tare da mutunta bangarorin da kundin tsarin mulki ya ba su iko.

Muhammadu Buhari, ya kuma yi kira ga rundunar sojin kasar ta samar da sabbin hanyoyin magance kalubalen tsaro na cikin gida.

Har ila yau, ya yi kira ga sojojin da aka yaye da daukacin sojoji kasar su ci gaba da kasancewa masu biyayya ga shugabansu yayin da suke gudanar da ayyukansu a cikin al'umma.

Ya kuma yabawa rundunonin sojin bisa ammana da suka yi da tsarin demokradiyyar kasar, wanda ya kai shekaru 18 a yanzu, ya na mai bukatar su sadaukar da kansu ga rantsuwar aiki da suka yi.

Sabbin Sojojin da ba za su gaza 600 ba, da suka hada da na kasa da na sama da kuma na ruwa ne aka yaye a matsayin laftanal na biyu wato second lieutenants. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China