in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya ta dauki wasu matakai na kawo karshen rikicin da ya barke a yankin kudancin kasar
2017-09-15 11:09:52 cri
Rundunar 'yan sanadan Nijeriya, ta dauki wasu dabaru na warware rikicin da ya barke a wasu sassan jihar Abia dake kudu maso gabashin kasar.

Babban Sufeton 'yan sandan Nijeriya Ibrahim Idris, wanda ya yi wa mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo bayanin game da rikicin, ya ce an dauki dabarun ne da nufin tabbatar da baza 'yan sanda a fadin kasar.

Ibrahim Idris ya kuma shaidawa manema labarai cewa, hukumomin tsaro na tuntubar Gwamnatin jihar, ya na mai cewa suna kokarin tattara shugabannin siyasa domin su shiga tsakani a inda ake da bukatar hakan, ta yadda za a rage zaman dar-dar da ake a yankin yanzu.

Ana zargin rikicin ya barke ne tsakanin wasu mambobin kungiyar dake rajin kafa kasar Biafra wato IPOB da al'ummar Hausa dake wasu sassan jihohin Abia da Rivers. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China