Shugaban karamar hukumar Bagudo Muhammade Zagga ya shaidawa maname labarai cewa, hadarin na jiya Alhamis ya faru ne lokacin da kwale-kwalen dauke da sama da fasinjoji 100 ya kife da dukkan mutanen dake cikinsa a tsakiyar ruwa, wadanda aka yi imanin cewa sun halaka. Sai dai har yanzu ana gudanar da aikin ceto ko da za a samu masu sauran numfashi.
Zagga ya kuma tabbatar da cewa, akwai 'yan kasuwa 53 galibinsu daga kauyen Gaya a Jamhuriyar Nijar cikin wadanda wannan hadari ya rutsa da su, a kan sanyarsu ta zuwa cin kasuwa.
Shugaba ya kuma ce hukumomin Jamhuriyar Nijar sun turo gwanayen linkaya don nemo wadanda suka bace.(Ibrahim)