in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi maraba da matakin Ghana na ba da viza ga 'yan kasashen mambobinta
2016-03-09 09:48:21 cri

Shugabar kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afrikan AU uwar gida Nkosazana Dlamini-Zuma, ta yi na'am da matakin da kasar Ghana ta bullo da shi na ba da takardun izinin shiga kasar ga al'ummomin kasashen mambobin kungiyar ta AU.

Shugaba John Dramani Mahama na kasar Ghana ne ya sanar da hakan a lokacin gabatar da jawabi a gaban majalisar dokokin kasar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

A jawabin nasa, Mahama ya fada cewar, daga watan Yulin bana, kasar Ghana ta amince ta baiwa 'yan kasashen mambobin kungiyar takardun izinin shiga kasar, inda da zarar sun shiga kasar, za su iya neman takardun na viza, idan har suna bukatar zama a kasar fiye da kwanaki 30, kuma za su iya cin moriyar abubuwan da kasar ta tanada.

Wannan mataki, a cewar Mahama, zai saukaka batutuwa da suka shafi sufurin jiragen sama da harkokin kasuwanci da zuba jari da kuma yawon bude ido.

Wannan mataki, ya biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma ne a yayin taron kungiyar ta AU cikin wannan shekara a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China