in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD da AU sun ratabba hannu kan yarjejeniya domin rigakafin barkewar rikici
2017-04-20 10:38:27 cri

Shugabannin MDD da na AU tarrayar Afrika sun rattaba hannu kan yarjejeniyar inganta hadin kai a tsakaninsu, da nufin kare aukuwar rikici da tabbatar da dorewar zaman lafiya a nahiyar Afrika.

A cewar yarjejeniyar da aka cimma a jiya, hukumomin biyu za su yi aiki tare, ta yadda za su rika musayar bayanai kan ainihin dalilan barkewar rikice-rikice da kuma yadda za a magance su.

Har ila yau, daftarin na bukatar bangarorin biyu su rika musayar bayanai da wuri, kan wuraren da ake tsammanin barkewar rikici da kuma yadda za a shirya tunkararsa.

Bugu da kari, hukumomin za su duba yiyuwar samar da kudade ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na tarayyar Afrika, karkashin shugabancin kwamitin sulhu na MDD.

Darakta janar na MDD Antonio Guterres ya shaidawa manema labarai cewa, manufofin iri guda da mara baya ga juna tsakanin hukumominsu da ake bukata a irin wannan lokaci za su tabbatar da dorewar zaman lafiya, da samar da ci gaba na bai daya tare da kare hakkin dan Adam.

Shugaban hukumar kula da ayyukan tarayyar Afrika Moussa Faki Mahamat ya ce, lokaci ya yi, da za a tantance jan kafa da ake yi da kuma karfin ayyukan wanzar da zaman lafiya a nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China