in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan MDD za ta tallafawa AU a fannin inganta ayyukan tsaro
2016-05-25 09:37:04 cri

Wakilin din din din na kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya yi kira ga MDD da ta dauki karin matakai, na tallafawa kungiyar tarayyar Afirka ta AU a fannin inganta ayyukan tsaro.

Mr. Liu wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, ya ce, daukar wannan mataki zai taimakawa nahiyar wajen wanzar da zaman lafiya da lumana. A cewar Liu Jieyi, hadin gwiwar MDD da kungiyar AU ya haifar da gagarumin ci gaba, kuma za a iya fadada hakan, idan aka inganta sha'anin horas da jami'ai, da samar da cibiyoyin horaswa, da kudaden gudanarwa da dai sauran su.

Bugu da kari, wakilin na Sin ya ce, kamata ya yi alakar dake tsakanin MDD da AU ta ci gaba da kasancewa bisa doron dokokin MDD, kana cudanyar sassan biyu, ta ci gaba da shafar bangarorin shawarwari, da shiga tsakani, tare da lura da hurumin kasashen na Afirka na ikon mulkin kai.

Daga nan sai Mr. Liu ya jaddada irin muhimmancin da kasar Sin ke dorawa, don gane da alakar ta da nahiyar Afirka, musamman a wannan fanni na kiyaye tsaro da wanzar da zaman lafiya. Yana mai cewa, tuni Sin ta shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya 16 a nahiyar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China