in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani harin kunar bakin wake ya halaka mutane 2 a Somaliya
2016-10-24 09:25:04 cri

Rahotanni daga Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya na cewa, wani 'dan kunar bakin wake ya halaka wasu mutane 2, kana wasu mutane hudu kuma suka jikkata bayan da ya tayar da bam din da ya dana a cikin mota da ya ke ciki.

Kwamishinan lardin Bondhere Qasim Abdullahi, ya shaidawa manema labarai a wurin da lamarin ya faru a yammacin jiya Lahadi cewa, maharin ya tayar da bam din da ke cikin motar tasa ce a wajen wani wurin cin abinci da ke kusa da wurin tarihi na Daljirka Dahsoon a lardin na Bondhere.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, fashewar tana da karfin gaske, kuma ta sanya mutane ranta cikin na kare.

Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar harin, amma kuma kungiyar Al-Shabaab tana kaddamar da hare-hare a kai a kai a cikin kasar, galibi a Mogadishu, babban birnin kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China