in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin gurneti ya hallaka mutane 3 a kudancin Somaliya
2016-12-13 09:20:32 cri

Wasu mahara da ba a tantance da ko su waye ba, sun hallaka mutane 3 tare da raunata wasu mutanen 7, bayan da suka jefa gurneti 2 kan wani dakin cin abinci dake birnin Kismayo, fadar mulkin jihar Jubaland dake kudancin kasar Somaliya.

'Yan sanda a birnin sun bayyana cewa, maharan sun jefa gurnetin biyu ne da almurun ranar Lahadi, da nufin hallaka dakarun sojin gwamnati dake cin abincin dare a lokacin.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da wannan hari, ko da yake a baya kungiyar Al-Shabaab ta sha kaddamar da makamantan wadannan hare hare a sassan kasar ta Somaliya. Harin na ranar Lahadi dai na zuwa ne 'yan sa'o'i, bayan aukuwar wani harin a birnin Mogadishu, wanda ya hallaka mutane 29.

A wani batun mai alaka da wannan kuma, kungiyar hadin kan Afirka ta AU, ta ce dakarun ta za su ci gaba da aiki tare da dakarun gwamnatin Somaliya, a wani mataki na murkushe ayyukan tada kayar baya da kungiyar Al-Shabaab ke aikatawa a daukacin sassan kasar ta Somaliya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China