in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin bam kan ofishin 'yan sandan Somalia ya yi sanadin mutuwar mutane 5
2017-06-23 10:16:36 cri

Wani harin bam da aka kai cikin mota a birnin Mogadishu na kasar Somalia, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Wannan hari dai shi ne na baya-bayan nan, cikin jerin hare-haren da aka kai birnin, a wannan lokacin da watan al'ummar musulmi na Ramadan ke shirin ban kwana.

Wata mota dauke da ababen fashewa ce ta kutsa ofishin 'yan sanda na Waberi jiya da rana.

Wannan na zuwa ne kasa da kwanaki biyu bayan an kai makamancin harin kan ofishin kwamsihinan lardi a Mogadishu, al'amarin da ya yi sanadin rayuka 10.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, sai da aka ji amon fashewar a gine-gine dake da dan nisa da inda aka kai harin, inda suka kara da cewa, nan take bayan kai harin ne aka rufe gidan rediyon Mustaqbal dake kusa da ofishin 'yan sandan.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, duk da cewa kungiyar Al-Shabaab ta dauki nauyin hare-hare biyu na baya da aka yi cikin mako guda, wadanda suka yi sanadin kimanin rayuka 40. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China