in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta bukaci mambobin EU su yi aiki wajen dage takunkumin da Amurka ta kakaba mata
2017-09-11 10:27:45 cri

Gwamnatin Sudan ta yi kira ga kasashen Tarayyar Turai, su yi aiki wajen ganin an dage takunkumin din din din da Amurka ta kakaba mata, kamar yadda aka tsara za a yi a watan Oktoba.

Ministan harkokin wajen Sudan Ibrahim Ghandour ya gana a jiya da shugaban tawagar EU a Sudan Jean-Michel Dumond, tare da jakadoji da wakilan Birtaniya da Italiya da Norway da Sweden da Jamus da Faransa da Spaniya da kuma Netherlands.

A karshen watan Yuli ne Amurka ta tsawaita lokacin nazari na watanni 3, domin yanke shawarar ko za ta dage takunkumin din dindin na cinikayya da ta kakabawa Sudan, la'akari da sakamakon da ta samu a fannin kare hakkin dan Adam da sauran batutuwa.

A kuma ranar 13 ga watan Junairun bana ne tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana matakin soke umarni biyu da ya bayar na sanyawa Sudan takunkumin tattalin arziki.

Umarnin shugaban ya ba da kwanaki 180 na nazari kafin dage takunkuman baki daya, don tabbatar da dorewar gwamnatin Sudan wajen kare hakkin dan Adam da yaki da ta'addanci.

Matakin ya kuma ba da damar komawa ga dukkan wasu harkokin banki da cinikayya tsakanin kasashen biyu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China