in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta tsawaita shirin tsakaita bude wuta zuwa watan Oktoba
2017-07-03 09:29:07 cri

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya sanar a ranar Lahadi cewa, ya amince da tsawaita wa'adin shirin tsakaita bude wuta a yankunan dake fama da rikici a kasar har zuwa watan Oktoba.

Sabon shirin tsakaita bude wutar zai yi aiki ne a yankunan Darfur da kudancin Kordofan da Blue Nile wadanda ke makwabtaka da Sudan ta kudu, wata majiya daga ofishin shugaban kasar Sudan din ce ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Sanarwar da gwamnatin Sudan ta fitar ta tsakaita bude wuta a watan Janairu, ta zo karshe ne a watan Yuni.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China