Kasar Sudan, ta ce a shirye ta ke ta ba da dukkan goyon baya da taimakon da zai kai ga rage jami'an wanzar da zaman lafiya na kawancen MDD da tarayyar Afrika da ke aiki a Darfur (UNAMID), bisa hadin gwiwar gamayyar kwamitoci da aka kafa domin aiwatar da shirin.
Ministan tsaro na Sudan Awad ibn Auf ne ya sanar da haka a jiya, bayan ganawa da karamin sakatare janar na MDD mai lura da ayyukan wanzar da zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix, wanda ya kai ziyara kasar domin nazarin yadda za a aiwatar da shawarar MDD ta rage dakarun UNAMID kamar yadda aka tsara. (Fa'iza Mustapha)