Hukumar sifiyon kasa ta Amurka ta ce, an samu girgizar kasa mai karfin maki takwas a yankin gabar ruwa dake kudancin Mexico a daren jiya Alhamis.
Girgizar da ta kai zurfin kilomita 33 ta mamaye kilo mita 96 na yankin kudu maso yammacin garin Pijijiapan na jihar Chiapas dake Mexico.
An ji girgizar a birnin Mexico, al'amarin da ya sa mutane tserewa daga cikin gine-gine zuwa kan titi.
Mutane sun ce, girgizar ta kai tsawon dakika 20, kuma tagogi da gadaje sun yi ta girgiza a lokacin. (Fa'iza Mustapha)