in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shehunan malamai sun yi kira da a samar da ingantaccen ilimi a Afrika
2017-07-06 09:16:23 cri

Shehunan malamai sun ce ya kamata burin samar da ingantaccen ilimi a nahiyar Afrika ya zama muhimmin batu da za a mai da hankali a kai.

Malaman sun bayyana haka ne yayin wani taron yini biyu dake da nufin wayar da kan masana, game da bukatar daga darajar ilimin gaba da sakandare, wanda aka fara a jiya a Kigali, babban birnin kasar Rwanda.

An shirya taron wanda zai shafe ranakun 5 da 6 ga wata, karkashin inuwar cibiyar tabbatar da muradun ci gaba masu dorewa ta Afrika, domin tattaunawa da samar da mafita, tare da cimma manufofin da suka dace da shirin aiwatar da muradun ci gaba masu dorewa a manyan makarantu da cibiyoyin bincike a Afrika.

A cewar shugaban kwalejin African Leadership Academy mai ba da horo kan shugabanci na gari Fred Swaniker, samar ingantaccen ilimi babban abun damuwa ne a Afrika, yana mai cewa, ilimi shi ne kashin bayan ci gaban tattalin arziki da zaman takewa.

Taron na yini biyu ya ja hankalin malamai da masana sama da 300 daga nahiyar Afrika da ma sauran sassan duniya.

A nasa bangaren, shugaban jami'ar Ibadan dake Nijeriya Abel Idowu Olayinka, ya ce kyakkyawan kudurin shugabanci zai magance matsalolin ilimi da ake fuskanta yanzu a Afrika, sannan zai ba kasashen nahiyar damar kirkiro dabarun samar da ingantaccen ilimi ga matasan Afrika.

Ya ce, ilimi shi ne jigon samun ci gaba mai dorewa, kuma abu ne mai muhimmanci ba matasa damar samun ilimi da fasahohi domin a samu dorewar ci gaba da kuma tunkarar matsalolin da suka shafi duniya baki daya.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China