in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana gayyatar kafafen yada labarai domin daukar rahoto yayin babban taron wakilan JKS karo na 19
2017-09-08 10:28:27 cri

An sanar da gayyatar 'yan jarida daga ciki da wajen kasar Sin, domin daukar rahoton babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis karo na 19 dake tafe.

Wata sanarwa a hukumance da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta ruwaito cewa, masu sha'awar daukar rahoto za su iya mika wasikar bukatar tsakanin ranakun 8 zuwa 25 ga wannan wata.

Yayin taron, wata cibiyar watsa labarai dake nan birnin Beijing, za ta shirya taron manema labarai da kuma hirraraki tsakanin jami'ai da 'yan jarida.

Za kuma a iya samun damar shiga shafukan yanar gizo da Wechat na cibiya.

Ana sa ran fara babban taron na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a ranar 18 ga watan Oktoba a nan birnin Beijing. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China