Wata kotu a kasar Habasha ta yankewa wani dan Nijeriya hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 7 saboda kama shi da ta yi da laifin boye hodar ibilis a cikinsa.
Hukumomin kasar ne suka kama Emeka Rapheal mai shekaru 36 da ya fito daga kasar Brazil zai tafi Nijeriya, a filin jirgin saman kasa da kasa na Bole dake birnin Addis Ababa, a lokacin da ya tsaya yada zango.
Na'urar bincike ta filin jirgin saman ce ta gano dauri 27 na hodar ibilis da nauyinsu ya kai gram 500 a cikin Emeka Rapheal.
Baya ga daurin na shekaru 7, babbar kotun tarayya ta Habasha, ta kuma ci Emeka tarar dala 370. (Fa'iza Mustapha)