in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an gwamnatin Habasha da 'yan kasuwa 34 sun gurfana gaban kotu bisa zargin cin hanci
2017-07-28 10:07:42 cri

Mutane 34 daga cikin manyan jami'an gwamnatin Habasha da 'yan kasuwa da masu shiga tsakani wajen kulla kasuwanci 37 da aka tsare a ranar Talata da ta gabata bisa zargin cin hanci, sun gurfana gaban kotun kasar a jiya Alhamis.

Mutanen 34 da ake zargi, sun gurfana gaban sashen hukunta manyan laifuka na biyu na babbar kotun Habasha, bisa zargin almundahanar sama da birr na kasar biliyon 2, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 86.

Yayin da mutanen suka nemi kotu ta ba su beli, rundunar 'yan sandan kasar ta nemi kotun ta kara mata kawanki 14 domin ta tattara shaidu, sannan ta hana mutanen beli, tana mai ikirarin cewa, idan aka ba su beli za su iya boye wasu takardu.

Kotun ta ba rundunar 'yan sandan karin kwanaki 14 da ta nema, kana ta dage sauraron shari'ar zuwa ranar 9 ga watan Agustan mai zuwa.

Tsare mutanen da aka yi wani bangare ne na garambawul da gwamnatin kasar ke yi, wanda aka fara a karshen 2016 domin samar da gamsasshiyar amsa ga damuwar al'umma. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China