in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar musulmin Habasha sun yi bikin karamar sallah
2017-06-26 11:03:59 cri

Al'ummar musulmin kasar Habasha, sun yi bikin sallah karama a jiya Lahadi, bayan da suka kammala ibadar azumin watan Ramadhan. Limanan kasar dai sun ja hankulan al'ummar musulmi da su rungumi dabi'ar zaman lafiya da lumana.

A birnin addis Ababa, tun da sanyin safiya dubban masallata suka yi fitar dango zuwa babban filin wasan kasar, inda aka gudanar da sallar idin ta baya.

Da yake tsakoci game da zagayowar wannan rana, shugaban majalissar addinin musulunci ta kasar Sheikh Muhammad-Amin Jamal Omar, ya ce Habasha kasa ce mai al'ummu da dama dake bin addinai mabanbanta. Wadda kuma ke rike da aki'dar zaman jituwa tsakanin su. Daga nan sai ya kara jan hankulan su, da su yi riko da wannan kyakkyawar dabi'a.

Sheikh Omar ya ce, ya zama wajibi, al'ummar musulmi su taka rawar da ta dace, domin wanzar da zaman lafiya da lumana a kasar su, tare da ba da gudummawar raya tattalin arzikin kasar baki daya.

Har ila yau ya yi kira ga 'yan kasar mazauna kasar Saudiyya ba bisa ka'ida ba, da su koma gida kafin kwanaki 90 na afuwa da aka ayyana.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China