in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya da AU na kokarin warware rikicin siyasar kasar
2017-06-01 09:29:55 cri

Firaministan Libya da MDD ke marawa baya, Faiz Sarraji ya gana a jiya Laraba, da tawagar kwamitin tarayya Afrika kan rikicin Libya, inda suka tattauna kan rikicin da ake karkashin yarjejeniyar siyasa.

Tawagar ta AU ta kunshi ministocin harkokin wajen kasashen Congo da Guinea da Niger da Mauritania da kuma kwamishinan kungiyar mai kula da harkokin wanzar da zaman lafiya da tsaro Ismail al-Sharqawi.

Tawagar ta kuma jadadda goyon bayan AU ga gwamnatin hadin kan kasar, tana mai jinjinawa kokarin da Faiz Sarraji ke yi na ganin ya sulhunta jam'iyyun siyasa masu adawa da juna.

A cewar tawagar, manufar taron ita ce, shigar da dukkan jam'iyyun siyasa cikin shirin tare da tattara ra'ayoyi mabanbanta wuri guda.

A nasa bangare, Faiz Sarraji ya yabawa goyon bayan da AU ke ba tsaron kasar, yana mai cewa, sulhun na bukatar kawo karshen goyon baya da masu ruwa da tsaki daga ketare ke ba jam'iyya guda, al'amarin da ya ce ya kara ta'azzara rikicin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China