in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Libya sun kwance nakiyoyi sama da 3,800 a Benghazi
2017-06-22 10:18:26 cri

Rundunar sojin Libya ta ce, ta kwance nakiyoyi sama da 3,800 da aka binne a tsakiyar Benghazi

Ofishin watsa labarai na rundunar ya kuma bayyana cewa, dakarun dauke da manyan makamai na ci gaba da kai farmaki kan kungiyoyin 'yan ta'adda a yankunan Al-Sabri da Suq Al-Hut dake tsakiyar Benghazi.

Benghazi dake yankin gabashin Libya kuma birni na biyu mafi girma a kasar da ya kasance mahaifar zanga-zangar da ta kai ga hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar a shekarar 2011, ya shafe shekaru 3 yana fama da rikice rikice tsakanin sojojin dake karkashin jagorancin Janar Khalifa Haftar da kungiyoyin tsageru.

Sojoji ne ke rike da yawancin sassan Benghazi, ban da wasu kananan yankuna dake tsakiyar birnin, inda ragowar tsageru ke zaune.

Dakarun Haftar ne ke rike da iko da gabobin da ake safarar man fetur dake gabashin kasar da galibin na kudanci, bayan sun yi galaba a kan kungiyoyi masu dauke da makamai.

Ofishin watsa labaran ya kuma bayyana cewa, dakarun na aiki cikin sirrri don samun nasara kan tsagerun, yana mai cewa, nakiyoyin ne suka hana su kwace iko da sauran yankunan na Benghazi. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China