in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin kasa da kasa na taimakawa wajen fitar da haramtattun kudade daga Afirka, in ji Mbeki
2015-05-22 10:03:14 cri

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Thabo Mbeki, ya zargi manyan kamfanonin kasa da kasa, da laifin taimakawa wajen fidda haramtattun kudade daga nahiyar Africa.

Mr. Mbeki ya ce, bisa alkaluman kididdiga, a ko wace shekara a kan yi safarar kudade ta barauniyar hanya, wadanda yawan su ya kai dala biliyan 50, kudaden da mafiya yawansu irin wadannan manyan kamfanoni ne ke tallafawa wajen fitar da su.

Tsohon shugaban wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin taro na 6, na dandalin hadin gwiwar majalissun dokokin kasashen Afirka a birnin Johannesburg, ya kara da cewa, wannan harka ta safarar haramtattun kudade na kassara ci gaban nahiyar Afirka.

Ya ce, fidda irin wadannan kudade masu yawa, abu ne da sam bai dace ba, duba da yadda hakan ke shafar nahiyar, wadda ke cikin matukar bukatar kudaden da za a yi amfani da su wajen ayyukan samar da ci gaba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China