in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika na bukatar inganta sarrafa kayayyaki domin cike gibin raguwar kudaden tallafi.
2017-09-07 10:50:00 cri
Mataimakin shugaban kasar Ghana Mahamudu Bawumia, ya ce idan har Afrika na son cike gibin raguwar kudaden tallafi da take samu daga kasashen da suka ci gaba, to akwai bukatar ta inganta kwazonta ta fannin sarrafa kayayyaki.

Mahamudu Bawumia ya ce za a cimma wannan buri ne idan bangarori masu zaman kansu na aiki yadda ya kamata, sannan aka cike gibin da ke akwai a fannin kayakin more rayuwa.

Mataimakin shugaban kasar wanda ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da mukala yayin taron yini daya, karon farko tsakanin ministocin G-20 ta kasashe masu karfin tattalin arziki da na kasashen Afrika, bisa Shirin tallafawa nahiyar Afirka da damammaki na zuba jari kungiyar karkashin kawancen bangarorin biyu na inganta zuba jari wato CWA, ya ce akwai bukatar kasashen Afrika su jajirce wajen inganta shirin CWA da managartan manufofi.

Ya ce shirin ya ba Ghana damar sake mai da hankali kan bangarorin da ke matsananciyar bukatar jari da kuma wadanda aka kyautata musu yanayin kasuwacin.

Manufar CWA ita ce, samar da nagartattun hanyoyin zuba jari a dukkan bangarori ga kowacce kasa tsakanin kasashen Afrika da hukumomin kasashen waje da sauran abokan hulda. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China