in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu ruwa da tsaki na fatan amfani da harkokin cinikayya wajen bunkasa yankunan tafkunan Afirka
2017-07-12 10:55:17 cri
Mahalarta wani taro na masu ruwa da tsaki game da ci gaban yankunan dake kewayen manyan tafkunan Afirka, sun yi fatan bullo da sabbin dabaru, na ciniki da kasuwanci, wadanda za su bada damar inganta tsaro da zaman lafiya a wannan yanki mai yawan fama da tashe tashen hankula.

Kaza lika yayin taron, an tattauna game da hanyoyin inganta rayuwar al'ummun wannan yanki, wadanda da yawa ke rasa muhallan su sakamakon rigingimu iri daban daban.

Dandalin samar da ci gaba da bunkasa harkokin cinikayya na MDD ko UNCTAD a takice, da hadin gwiwar ofishin wakilin musamman na babban magatakardar MDD game da yankin manyan tafkunan na Afirka ne suka shirya taron a jiya Talata.

Cikin mahalarta taron dai hadda babban sakataren UNCTAD Mukhisa Kituyi, da mataimaki na samuamman ga babban magatakardar MDD Said Djinnit. Wadannan jami'ai biyu sun tabo batu game da matakan da taron birnin Geneva ya zayyana na bunkasa hada hadar cinikayya, da ma irin tasirin su, warware matsaloli masu sarkakiya da al'ummun sassan duniya ke fuskanta.

Da yake tsokaci game da hakan Mr. Mukhisa Kituyi, ya ce yankin tafkunan Afirka na da sama da mutane miliyan 7, wadanda ke rasa muhallansu, da kuma 'yan gudun hijira kusan miliyan 3.5.

A nasa bangare kuwa, Mr. Said Djinnit, cewa ya yi ya zama wajibi, a gwama matakan siyasa da sauran dabaru, domin dawo da wannan yanki cikin hayyacin sa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China