in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cibiyoyin Afrika sun bayyana tasirin da alkaluman bincike ke yi ga cigaban muradun karni
2017-07-23 13:47:50 cri

Manyan daraktocin cibiyoyin kididdiga (NSI) na kasashen Afrika 40, sun nanata muhimmancin da alkaluman da cibiyoyin bincike ke fitarwa wajen cimma nasarar shirin muradun karni.

Cikin takardar yarjejeniya da aka fitar bayan kammmal taron alkaluman kididdiga na duniya (WSC) karo na 61, wanda ya gudana tsakanin 16 zuwa 21 ga watan nan na Yuli a Marrakech, cibiyoyin na Afrika sun nanata muhimmancin cigaba da yin nazari don samar da alkaluman, da bibiya da kuma nazartar yadda ake aiwatar da dukkan manufofin cigaba bisa dukkan burikan da kasashensu ke son cimmawa.

Sanarwar ta kara da cewa, alkaluman binciken da ake fitarwa, da musayar ilmi tsakanin kasashen Afrika za su taimaka musu wajen cimma nasarar shirin muradun ajadar dawwamamman cigaba nan da shekarar 2063 na Afrika, da kuma na cigaban muradun karni na shekarar 2030, kana da kuma cimma nasarar yarjejeniyar Paris daidai da wa'adin da aka cimma matsaya a kansa, da nufin mayar da shirye-shiryen wasu muhimman ginshikan tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki da yanayin zamatakewar al'ummar nahiyar ta Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China