in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ba ta fuskantar karancin abinci, in ji ministan ma'aikatar gona
2017-09-06 10:17:22 cri

Ministan ma'aikatar gona da raya karkara a tarayyar Najeriya Audu Obbeh, ya ce ko alama Najeriya ba ta fuskantar matsalar karancin abinci, duk kuwa da bullawar wasu tsutsotsi da suka yiwa amfanin gona barna a wasu sassan kasar.

Mr. Ogbeh, wanda ya bayyana hakan a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriyar, ya ce tsutsotsin sun yi barna a gonakin jihohin kasar da dama, amma hakan ba zai haifar da karancin abinci ba a kasuwanni.

Ministan ya yi wannan tsokaci ne yayin wani taron bunkasa sanin makamar aiki, na jami'an kasashe mambobin kungiyar bunkasa tattalin arzikin yammacin Afirka ta ECOWAS, game da yaki da halittu masu lalata amfanin gona.

Ya ce, cikin dalilan da suke haddasa hauhawar farashin kayayyakin abinci a Najeriya, akwai rashin ingancin hanyoyin fitar da abincin zuwa kasuwanni. Daga nan sai ya yi kira ga 'yan Najeriya da kada su damu, duba da cewa gwamnati ta fara samun tallafi daga hukumomin kasa da kasa, a fannin dakile annobar tsutsotsin dake lalata amfanin gona.

Hukumar abinci da aikin gona ta MDD FAO ce dai ta shirya wannan taro, da hadin gwiwar wasu kasashen Afirka 15.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China