in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin baje kolin kayan fasahohin hannu na Afirka a Najeriya
2017-09-06 09:38:04 cri

A jiya Talata ne aka bude wani kasaitaccen bikin baje kolin kayan fasahohin hannu na al'ummun nahiyar Afirka, a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya, bikin da ya samu halartar kasashen nahiyar 17, da kuma wakilan jihohin Najeriya 26.

Rahotanni na cewa, bikin nune nunen na bana, shi ne irin sa mafi girma da hukumar bunkasa al'adu da fasahohin hannu ta Najeriyar NCAC ta taba shiryawa.

Yayin bikin budewar, an nuna wasannin gargajiyar al'ummu daban daban na Najeriya. Bikin ya kuma samu halartar baki daga kasashen ketare da dama, da wakilan ofisoshin jakadanci, baya ga jami'ai daga hukumomin kasar, tare kuma da masu nuna fasahohi daban daban.

An dai fara bikin ne tun daga shekarar 2008, kuma a duk shekara yana janyo baki daga kasashen Afirka, da ma na ketaren nahiyar da dama.

Da yake bayyana muhimmancin sa, shugaban hukumar NCAC Segun Runsewe, ya ce gwamnatin kasar mai ci, na fatan amfani da harkar raya al'adu a matsayin hanyar bunkasa tattalin arziki, maimakon dogaro kacokan ga cinikayyar danyen mai.

Mr. Runsewe ya kara da cewa, bikin da ake gudanarwa mai kayatarwar gaske, na hade sassan al'ummun Afirka dake da sha'awar fasahohin gargajiya, tare da budewa Najeriya wata kafa, ta bayyanawa duniya fasahohin ta.

Cikin al'ummun da suka baje basirar su a bikin na bana dai akwai 'yan kasar Kamaru, da Senegal, da Gambia, da ma wasu kasashe daga tsakiyar nahiyar Afirka.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China