in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Najeriya ya fita daga matsanancin hali
2017-09-06 09:17:15 cri

Wasu alkaluma da ofishin hukumar kididdiga na tarayyar Najeriya ya fitar sun nuna dewa, kasar ta fita daga matsin tattalin arziki mafi muni da tsunduma, wanda ba a taba ganin irin sa ba cikin shekaru 20 da suka gabata.

Alkaluman sun nuna cewa, Najeriya ta samu karuwar kaso 0.55 bisa dari na ci gaba, a watanni 3 na biyu na wannan shekarar ta 2017 da muke ciki. Kafin hakan kasar na da gibin kaso 0.91 bisa dari ne a watanni 3 na farkon shekarar ta bana. Kaza lika ta fuskanci gibin kaso 1.49 a watanni 3 na biyu na shekarar bara.

Alkaluman sun kuma bayyana cewa, Najeriya ta fita daga komadar tattalin arziki a wannan gaba ne, sakamakon hobbasa da aka yi a fannin raya harkokin noma, da da cinikayyar danyen mai, da fannin masana'antu, da kuma harkokin cinikayya.

Gwamnatin Najeriya dai na aiki tukuru a bangaren hade sassan ci gaban ta, bayan da ta tsunduma cikin matsin tattalin arziki tun daga watanni ukun farko na shekarar bara.

Tuni dai shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayyana fitar kasar daga mawuyacin halin tattalin arziki, yayin da yake zantawa da takwaransa na Janhuriyar Nijar a jiya Talata a fadar gwamnatin kasar dake birnin Abuja. Ya ce, babbar nasarar hakan za ta bayyana karara, bayan da talaka ya fara gani a kasa.

Bugu da kari, fadar gwamnatin Najeriyar ta fidda wata sanarwa, mai dauke da sa hannun kakakin shugaban kasar Laolu Akande, wadda ke cewa gwamanati na yin iyakacin kokari, don ganin ta cimma nasarar bunkasa tattalin arziki, tare da fadada hanyoyin samun kudaden shiga, da samar da guraben ayyukan yi, tare da bunkasa yanayin cinikayya da sana'o'i tsakanin al'ummun kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China