Hukumar yaki da masu fatauci da ta'ammali da miyagun kwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta ce, jami'anta sun yi nasarar damke wasu da ake zaton dillalan miyagun kwayoyi ne su goma a jihar Adamawa dake yankin arewa maso gabashin kasar.
Kwamandan hukumar ta NDLEA dake jihar Wale Ige ya shaidawa manema labarai a Yole, fadar mulkin jihar Adamawa cewa, an kama wadanda ake zargin ne a cikin makon da ya gabata, biyo bayan sabbin matakan yaki da dillalan miyagun kwayoyi da hukumar ta fara aiwatarwa a fadin jihar, da nufin kakkabe dillalan miyagun dake kokarin bata rayuwar matasan jihar da miyagun kwayoyi.(Ibrahim)