in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya yi kira da bada kariya ga fararen hula da masu aikin agaji da rikici ya rutsa da su
2017-08-19 11:34:29 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da hare-hare kan fararen hula da masu aikin agaji a wuraren da ake rikici, yana mai kira da a ba su kariya.

Antonioa Guterres ya yi wannan kira ne yayin bikin ranar agajin jin kai ta duniya dake gudana a ranar 19 ga watan Augusta.

Ya ce kare fararen hula a lokacin rikici abu ne mai wahalar aiwatarwa. Sannan abu mafi muni shi ne yadda ake kara kai hare-hare kan masu bada agajin jin kai, baya ga rashin darajar tutar Majalisar, wanda alama ce dake nuna cewa ba ta nuna fifiko ga wani bangare dake rikici.

Har ila yau, Sakataren na MDD ya ce kare fararen hula yayin da ake rikici muhimmin abu ne cikin dokar agajin jin kai ta duniya. Sai dai, a fagen yaki a duk fadin duniya, bangarorin dake rikici na take wannan doka, inda ake ci gaba da kai hare-hare tare da kashe fararen hula, yana mai cewa, ba a dauki ran dan Adam a bakin komai ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China