Zeid ya bayyana cewa, tun bayan da Trump ya hau kan kujerar shugabancin kasar Amurka, yake zargin kafofin watsa labaru har ma a wasu lokutan ya kan kira su da sunan mazambata. Koda a makon da ya gabata yayin da shugaba Trump ya ziyarci jihar Arizona, ya kira 'yan jarida a matsayin marasa gaskiya kana makiyan kasar Amurka. Zeid ya yi kashedi cewa, Trump ya sha zargin kafofin watsa labaru da nuna musu kiyayya, kuma hakan a cewarsa zai haddasa rikici ga 'yan jarida.
Hakazalika, Zeid ya ce, 'yancin watsa labaru yana cikin kundin tsarin mulkin kasar Amurka, kuma wannan shi ne abin da kasar ta Amurka take kokarin tabbatarwa a shekaru da dama da suka gabata. Amma yanzu shugaban kasar yana adawa da wannan manufa, kuma wannan ba abu ne mai kyau ba kuma babban hadari ne ga kasar baki daya. (Zainab Zhang)