A jiya ne, ofishin jakadancin Amurka dake Rasha ya ce, saboda karancin ma'aikata, ofishin zai dakatar da baiwa Rashawa 'yan kasuwa, da dalibai, da masu yawon bude ido takardar iznin shiga kasar a duk fadin Rasha tun daga gobe 23 ga wata. Kana, daga ranar 1 ga wata mai zuwa, ofishin jakadancin Amurka dake Rasha zai dawo da jarrabawar da aka saba yiwa Rashawa 'yan kasuwa, da dalibai da masu yawon bude ido wadanda suke son samun takardar iznin shiga Amurka, amma wasu kananan ofisoshin jakadancin Amurka dake Rasha guda uku, za su dakatar da ba da takardar shiga Amurkar har Illah Masha Allahu.(Murtala Zhang)