in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana makokin mutanen suka mutu sanadiyyar zaftarewar kasa a Habasha
2017-03-16 09:28:27 cri

Kasar Habasha ta fara zaman makoki na kwanaki uku, domin alhinin mutuwar mutane da adadinsu ya kai 113, sanadiyyar zaftarewar wata bola dake wajen Addis Ababa, babban birnin kasar.

A jiya Laraba ne kasar dake gabashin Afrika ta yi kasa-kasa da tutocinta zuwa rabi, domin alhinin mutuwar mutanen da al'amarin ya rutsa da galibinsu ke cikin gidajensu a lokacin da bolar mai fadin hectare 36 ta zaftare.

Shugaban sashen yada labarai na hukumar kula da birnin Addis Ababa Dagmawit Moges, ya ce an gano karin gawarwaki 41, inda adadin a yanzu ya kai 113

Har yanzu jami'ai a yankin ba su da tabbacin adadin wadanda zaftarewar bolar ta rutsa da su, inda suka ce, ta yiwu a kuma samun karin gawarwaki yayin da ake ci gaba da bincike ba dare-ba-rana a yankin bolar da ake kira da Koshe

Gwamnati ta kwashe mutane 320 dake zaune a yankin zuwa wani wuri na daban. Haka zalika, an kafa kwamitin da aka dorawa alhakin kai dauki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China