in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da littafin shugaba Xi kan rage talauci cikin harsunan Turanci da Faransanci
2017-08-24 13:16:44 cri

An kaddamar da littafin shugaban kasar Sin Xi Jinping kan dabarun rage talauci cikin harsunan Turanci da Faransanci, a jiya Laraba yayin baje kolin littafai na duniya karo na 24 dake gudana.

Littafin mai suna "Up and out of Poverty" ya kunshi mukalun da jawaban shugaba Xi guda 29, tare da hotunansa tun daga shekarar 1988 zuwa 1990, a lokacin da yake shugaban jam'iyya a birnin Ningde dake lardin Fujian na gabashin kasar Sin.

Mataimakin sashen kula da labarai da wallafe-wallafe da kafafen rediyo da talabijin na kasar Wu Shangzhi, ya ce kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis dake da shugaba Xi a matsayin jigo, ya dauki batun rage talauci a matsayin tubalin gina al'umma mai matsakaicin ci gaba.

Ya ce, matakin da kasar Sin ta dauka zai zama abun koyi ga sauran kasashe wajen fatattakar talauci.

Littafan da aka yi cikin harsunan kasashen waje, sun jawo hankali tare da samun jinjina daga 'yan siyasa da malamai da kafafen yada labaran kasashen Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China