in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sayar da littafin game da sha'anin mulkin shugaba Xi sama da kwafe miliyan 6 a duniya
2017-08-24 13:07:23 cri

Adadin kwafen littafi game da salon mulkin shugaban kasar Sin Xi Jinping cikin harsuna 21 da aka sayar da su a ciki da wajen kasar Sin ya kai miliyan 6.42.

Littafin mai suna "Xi Jinping: The Governance of China" wato, Xi Jinping yadda yake jagoranta mulkin kasar Sin, an yi baje kolin littafin ne a lokacin bikin baje kolin littattafai na kasa da kasa na Beijing karo na 24, wanda aka bude a ranar jiya Laraba, kuma an sayar da littattafan ne a kasashen duniya da yankuna sama da 160, tun daga lokacin kaddamar da littafin a watan Satumbar shekarar 2014.

Littafin yana kunshe da jawabai, laccoci, tattaunawa, da wasiku kimanin 79, wanda shugaban kasar Sin ya gabatar tsakanin watan Nuwambar shekarar 2012 zuwa watan Yunin shekarar 2014.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China