Shugaban sashin kula da ka'idoji da dokokin shari'a na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mista Xu Hong ya jagoranci tawagar gwamnatin kasar Sin don halartar taron.
A cikin jawabin da ya gabatar, Xu Hong ya ce, gwamnatin kasar Sin na maida hankali sosai kan raya dokokin shari'a a fadin duniya, da nuna hazaka wajen shiga harkokin kungiyoyin kasa da kasa da na shiyya-shiyya. Haka kuma kasashen Asiya da na Afirka suna taka muhimmiyar rawa wajen kiyayewa gami da raya dokokin shari'a a fadin duniya. Kasar Sin na fatan yin hadin-gwiwa tare da kasashen Asiya da na Afrika, domin tabbatar da adalci yayin da ake amfani da dokokin shari'a a duniya.
An kafa kwamitin shari'a na tuntuba na Asiya da Afrika wato Asian-African Legal Consultative Organization ko kuma AALCO a shekara ta 1956, yanzu tana da kasashe membobi 47 gami da kasashe 'yan kallo guda biyu.(Murtala Zhang)