in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya bukaci a kwantar da hankula bayan barkewar rikicin bayan zaben Kenya
2017-08-13 11:53:07 cri
Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, a jiya Asabar, ya bukaci shugabannin adawar kasar Kenya da su yi kokarin yayyafa wutar rikicin da ya kaure a kasar bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasar, ya nemi su kalubalanci zaben ta hanyar matakin shari'a.

Sakatare janar din ya bayyana hakan ne bayan bayyana sakamakon zaben shugaban kasar na ranar Talata, inda hukumomin zaben kasar Kenyan suka ayyana shugaban kasar mai ci Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben.

Guterres, ya bukaci shugabannin siyasar kasar da su gaggauta yin kira ga magoya bayansu da su datakar da tashin hankalin. Sakatare janar din ya nanata muhimmancin tattaunawar sulhu domin kawo karshen zaman tankiya a kasar.

MDD, da kungiyar tarayyar Afrika, da sauran abokan hulda, sun tsaya tsayin daka inda suke gudanar da aiki tare da masu ruwa da tsaki da shugabannin siyasar kasar Kenyan domin tabbatar da ganin an aiwatar da zaben kasar cikin nasara.

An kashe mutane a kalla 20 a rikicin bayan zaben kasar ta Kenya sakamakon zargin da bangaren 'yan adawar kasar ke yi na tafka magudi a zaben inda suke zargin an fifita bangaren mista Kenyatta.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China