in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD ta damu game da ayyukan masu ta da kayar baya a yankin Sahel
2017-08-16 09:21:25 cri
Mataimaki na musamman ga babban magatakardar MDD game da ayyukan wanzar da zaman lafiya El-Ghassim Wane, ya yi wa kwamitin tsaron MDD karin haske, don gane da illar dake tattare da ayyukan masu ta da kayar baya a yankin Sahel.

Mr. Wane wanda ya gabatar da jawabi gaban zauren kwamitin na tsaron MDD a jiya Talata, ya ce yanzu haka tawagar hadin gwiwa ta dakarun kungiyar kasashen yankin na Sahel ta G5, wadda ta kunshi sojojin kasashen Mali, da Mauritania, da Nijar, da Burkina Faso da Chadi, na iyakacin kokarin murkushe ayyukan mayakan sa kai a yankin.

To sai dai kuma a cewarsa, ayyukan 'yan ta'adda na haifar da babban kalubale a yankin, kuma alakar bangarorin irin wadannan kungiyoyi da juna, na haifar da barazanar rashin daidaito, da ci gaban yankin baki daya.

A daya bangaren kuma a cewar jami'in, hadin gwiwar G5, ya bude wata kofa ta magance tarin kalubalen da wannan yanki ke fuskanta, inda shirin kungiyar ke samar da kudade, da dakaru, da horo da kayayyakin aiki da dai sauran su.

A ranar 2 ga watan Yuli ne shugabannin kungiyar ta G5, da hadin gwiwar kasar Faransa, suka kaddamar da rundunar musamman domin cimma burin wanzar da zaman lafiya da lumana a daukacin yankin na Sahel. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China