in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan wadanda suka rasu sakamakon harin kasar Sifaniya sun kai mutane 14
2017-08-18 20:37:10 cri

Yanzu haka yawan mutanen da suka rasu sakamakon tagwayen hare hare da suka auku a ranar Alhamis a Sifaniya sun karu zuwa 14, bayan da wata mace da ta samu raunuka ta rasu a wani asibiti dake Catalan a Jumm'ar nan.

Matar dai ta samu raunuka ne a harin Cambrils kamar yadda wasu sakwanni da aka wallafa ta shafin tweeter suka bayyana.

Matar na tare da wasu mutum 5, wadanda suka samu raunuka, lokacin da wata motar dakon kaya ta kutsa kai cikin dandazon mutane a wani filin shakatawa dake Cambrils, wurin da ke da nisan kilomita 100 daga kudu maso yammacin birnin Barcelona.

Yayin hari na biyu wanda ya auku a titin Las Ramblas, mutane 13 sun rasa ran su kana wasu sama da 100 suka jikkata lokacin da wata mota ta take masu tafiya a kafa a gefen wata hanya.

A wani ci gaban kuma, 'yan sanda a Catalan sun hallaka dukkanin wadanda ake zargi da kitsa wannan hari su 5, yayin wani bata kasha da suka yi da wasu masu dauke da wukake. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China