in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya mika sakon ta'aziyya game da rasuwar mutane a harin Barcelona
2017-08-18 19:18:16 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gabatar da sakon ta'aziyya game da rasuwar mutane da dama tare da jikkatar wasu a harin tsakiyar birnin Barcelona. Mr. Li Keqiang wanda ya gabatar da sakon ga takwaran sa na kasar Sifaniya Mariano Rajoy, ya yiwa iyalan wadanda suka rasu ta'aziyya a madadin gwamnatin kasar Sin, da kuma fatan samun sauki da wadanda suka jikkata.

Ya ce kasar Sin na goyon bayan Sifaniya wajen yaki da ta'addanci, za kuma ta gudanar da hadin gwiwa da dukkanin kasashen duniya ciki hadda Sifaniya a wannan fanni, ta yadda za a kai ga samar da al'ummar duniya mai rayuwa cikin yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China