in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya mika sakon ta'aziyya game da rasuwar mutane a harin Barcelona
2017-08-18 19:17:27 cri

A Juma'ar nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon ta'aziyya ga sarkin kasar Sifaniya Felipe VI, bisa rasuwar mutane a kalla 14, yayin da kuma wasu sama da 100 suka jikkata, biyowa bayan harin ta'addanci da ya auku a kasar.

Cikin sakon na shugaba Xi, ya bayyana matukar kaduwa da jin aukuwar wannan hari, ya ce a madadin gwamnati da al'ummar kasar Sin da shi kan sa, yana gabatar da sakon ta'aziyyar sa ga iyalai da 'yan uwan mamatan, yana mai fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata. Kaza lika shugaban na Sin ya jaddada aniyar sa, ta ci gaba da baiwa hadin gwiwar yaki da ta'addanci goyon baya, ta yadda za a kai ga samar da yanayi na wanzuwar zaman lafiya da lumana a dukkanin fadin duniya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China