Mr Ken Berlin wanda ya yi wannan yabo yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a gefen taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa, wanda shirin raya kasashe na MDD ya shirya, ya kuma yi gargadin cewa, ficewar Amurka daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, tana iya yin illa ga tattalin arzikin Amurkar.
Jami'in, ya ce kasar Sin tana nuna kyakkyawan shugabanci a duniya, kana tana kan turbar da ta dace a wannan fanni, a hannu guda kuma ya shawarce ta da ta rage dogara a kan makamashin kwal. Ya ce gwamnatin kasar Sin tana daukar managartan matakai a kokarin da take na magance matsalar sauyin yanayi, inda ya ba da misali da shirin shekaru biyar-biyar da mahukuntan kasar suka tsara game da raya makamashin da ake iya sabuntawa. (Ibrahim Yaya)